Isa ga babban shafi
G20

G20 : Manyan biranen duniya na son a mutunta yarjejeniyar Paris

Magadan garin manyan biranen kasashen dunya sun bukaci shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da su tsaya-tsayin daka don kare yarjejeniyar dumamayar yanayi da aka kulla a bara a birnin Paris, bayan Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar.

A Jamus an yi zanga-zangar adawa da ficewar Amurka daga yarjejeniyar canjin yanayi ta Paris
A Jamus an yi zanga-zangar adawa da ficewar Amurka daga yarjejeniyar canjin yanayi ta Paris REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Magadan garin sun yi wannan kira ne a jiya bayan kammala wani taro a birnin Paris na Faransa.

Magadan gari daga Washington da Paris da Berlin da Tokyo da Madrid da kuma Sydney na daga cikin wadanda suka yi kiran kafin taron shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya da za a gudanar daga 7 zuwa 8 ga watan Yuli a birnin Hamburg na kasar Jamus.

Magadan garin biranen Karachi da Montreal da Rio de Janeiro da Melbourne da Chicago da Warsaw da Seoul da kuma Vancouver na daga cikin sauran biranen da suka yi kiran.

Kiran na biranen ya ce bayan janjewar Amurka daga yarjejeniyar, a yanzu duniya ta zura wa sauran kasashe 19 ido ne domin ganin irin matakin da za su dauka kan batun na dumamar yanayi.

Magadan gari daga manyan biranen duniya 40 karkashin jagorancin takwararsu ta birnin Paris Anne Hidalgo, sun jinjina wa takwarorinsu na birane 300 na kasar Amurka, wadanda suka ce za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar Paris duk kuwa da matakin da Donald Trump ya dauka.

A farkon wannan wata na Yuni ne Trump ya yi watsi da yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma a watan disambar bara, saboda a cewarsa matukar Amurka ta ce za ta mutunta abubuwan da ke kunshe a cikinta, hakan zai shafi tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.