Isa ga babban shafi
Amurka-China

Safarar dan adam ta fi muni a China - Amurka

Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana China, Sudan da kuma Korea ta Arewa, a matsayin kasashen dake sahun gaba wajen safarar dan adama a fadin duniya.

Gungun wasu masu safarar mutane da jami'an tsaron kasar Thailand suka kama a birnin Bangkok.
Gungun wasu masu safarar mutane da jami'an tsaron kasar Thailand suka kama a birnin Bangkok. ©REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Cikin sabon rahoton da ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar, ya ce al’amarin ya fi muni a kasar China, kuma hukumomin kasar basa tabuka wani abun zo a gani domin yakar matsalar, ko kuma kare hakkin wadanda suka fada cikin matsalar.

A cewar rahoton ana matukar muzgunawa kabilar Uighur, dake da musulmi ‘yan kalilan a yammacin China, ga kuma batun korar ‘yan Korea ta Arewa ba tare da tantance ko akwai wadanda aka yi safarar su ba.

Rahoton wanda sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya kaddamar, ya kasance karo na farko da Gwamnatin Donald Trump ta soki gwamnatin China a kan batun hakkin bil’adama.

A nahiyar Africa kuwa rahoton ya yi tur da safarar dan adam a kasashen Janhuriyar Congo, Guinea da Mali yayinda lamarin yafi muni a kasashen Rasha, Iran, Syria da kuma Venezuela.

A cewar rahoton, kusan mutane miliyan 20 ne ake safarasu a fadin duniya tare da tilasta musu ayyukan wahala da kuma yin lalata da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.