Isa ga babban shafi
FAO

Bukatar abinci da kayan gona zai ragu a cikin shekaru 10

Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto wanda ke cewa bukatar abinci da kayan gona zai ragu a cikin shekaru 10 masu zuwa sakamakon raguwar bukatar haka daga China.

Bukatar abinci da kayan gona zai ragu a cikin shekaru 10
Bukatar abinci da kayan gona zai ragu a cikin shekaru 10 Laurent Correau / RFI
Talla

Rahotan Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce daga wannan shekara zuwa shekaru 10 nan gaba, za’a samu koma bayan bukatar amfanin gona sabanin yadda aka saba gani a shekaru 10 da suka gabata.

Rahotan hadin guiwar da hukumar da kuma takwarar ta Tattalin arziki da hadin kai suka wallafa, ya yi hasashen haka ne a kasashe 34 da suka fi habakar tattalin arziki daga yanzu zuwa shekarar 2026.

Daya daga cikin hujjojin da rahotan ya bayar shine raguwar bukatar abincin daga China, kasar da tafi yawan jama’a, wanda ya dangata shi da matsalar samun kudade wadanda zasu shafi sayen amfanin gonar.

Kasar China ta yi zarra wajen bukatar amfanin gona a cikin shekaru 10 da suka gabata, musamman abinda ya shafi nama da kifi.

Rahotan ya kuma ce, matsalar zata kuma shafi cinikin masara da rake da kayan marmari wadanda ake amfani da su yanzu haka wajen samar da man fetur.

Sai dai rahotan ya yi gargadin cewar duk da wannan tsaiko da za’a fuskanta matsalar samar da abincin da za’a ci zai ci gaba da zama babban kalubale ga kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.