Isa ga babban shafi
WHO

Yara da dama ba su samu allurar riga-kafi a 2016 ba- WHO

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce yaro daya a cikin dukkanin yara 10 na duniya bai samu karbar riga-kafin allurar cutuka masu yaduwa a shekarar da ta gabata ba. Lamarin da a cewar hukumar ya kawo mayar da adadin yaran da ba su karbi rigakafin ba zuwa su miliyan 13 a duniya baki daya.

Adadin yaran da ke samun cikakken rigakafi ya tsaya cak da kimanin kashi 86 cikin 100  a cewar WHO
Adadin yaran da ke samun cikakken rigakafi ya tsaya cak da kimanin kashi 86 cikin 100 a cewar WHO RFI/Guillaume Thibault
Talla

Rahotan hukumar ta WHO da hadin gwiwar asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya nuna cewa akwai kuma Karin yara sama da miliyan 6 da rabi wadanda suma ba su samu wani nau’in rigakafi da ake kira DTP ba.

Rahoton ya ci gaba da cewa tun shekarar 2010, adadin yaran da ke samun cikakken rigakafi ya tsaya cak da kimanin kashi 86 cikin 100, haka kuma yaran ba su samun cikakkiyar kulawar lafiyar da ta dace.

A cewar Jami’ar da ke kula da rigakafi a Hukumar ta WHO Jean-Marie Okwo-Bele, daga cikin kasashe 194 na Majalisar Dinkin Duniya, kasashe 130 ne kadai suka samu kashi 90 na rigakafin kananan yara.

Haka kuma kasashe irin su Najeriya da Somalia da Sudan ta kudu da Syria da Chadi da Equatorial Guinea da Afrika ta Tsakiya da Syria da Ukraine sun samu kaso 50 ne kadai na rigakafin kananan yaran.

Hukumar lafiyar ta duniya WHO dai ta kiyasta cewa ba wa yara rigakafin yadda ya kamata na taimakawa wajen hana mutuwar akalla yara milyan biyu zuwa uku a kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.