Isa ga babban shafi
Amurka-Koriya ta Kudu

Amurka na atisayen soji don razana Koriya ta Arewa

Kasashen Amurka da Koriya Ta Kudu na gudanar da atisayen soji da ya kunshi harba makamai masu linzami daga wannan sashi zuwa wancan  don razana Koriya ta Arewa da ta yi sabon gwajin makami mai linzami.

Koriya Ta Arewa ta yi sabon gwajin makami mai linzami
Koriya Ta Arewa ta yi sabon gwajin makami mai linzami KCNA/via REUTERS
Talla

Sai dai Koriya ta Arewa ta yaba da nasarar da ta samu a sabon gwajin mai cin dogon zango, abin da ta ce, gargadi ne ga Amurka.

Shugaban kasar, Kim Jong-un ya ce, gwajin na baya-bayan nan ya nuna cewa, dukkanin Amurka na cikin da’irar da hari zai shafa

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gwajin a matsayin hatsari, yayin da China ta soki matakin, in da kuma ta bukaci bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.

Faransa ta bukaci mambobin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su gaggauta kara kakaba wa Koriya Ta Arewa takunkumi bisa gwajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.