Isa ga babban shafi
Iran

Iran za ta ci gaba da kera makami mai linzami

Kasar Iran ta ce, ba ta da niyyar dakatar da shirinta na kera makamai masu linzami, duk kuwa da sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba ma ta. Ko a karshen makon da ya gabata, Iran ta yi gwajin wani makami mai linzami da ke cin dogon zango, matakin da gwamnatin Amurka ta bayyana matukar damuwarta a kai.

Iran ta yi gwajin wani makami mai linzame da ke cin dogon zango a karshen mako
Iran ta yi gwajin wani makami mai linzame da ke cin dogon zango a karshen mako REUTERS/Tasnim News Agency
Talla

Iran dai kasa ce da ta mallaki makamai masu linzami iri daban daban, da suka hada da samfurin, Ghar da kuma Sinjil da kowanne ke iya cin sama da kilomita dubu biyu,  idan aka harba shi, wanda zai iya fadawa a cikin Isra’ila ko kuma kan bataliyoyin sojin Amurka da ke yankin.

Akwai wani makami mai suna Imad, wanda shi ne na farko da Iran ta yi gwaji tun bayan kulla yarjejeniyar Nukiliya da kasashen duniya a 2015, yayin da kasar ta sayo wata na’urar kariya daga makamai masu linzami samfurin S-300 daga Rasha.

To sai dai kafin wata na’urar kasar Rasha, tuni Iran ta sanar da kerawa kanta wani makamin mai suna Bavar-373 wanda rundunar tsaron kasar ke cewa ya fi na Rashan inganci.

A halin yanzu dai, ba wanda ya san adadin makamai masu linzami da kuma karfin zangonsu wadanda Iran ta mallaka, to sai dai wani lokaci a baya, kasar ta yi gwajin wani makami mai cin gajeren zango da ake kira Sayyad na uku, yayin da akwai wasu dimbin makaman da ake harbawa daga tudu zuwa ruwa, ko cikin sararin samaniya, yayin da kasar ta mallaki wasu makaman da ake harbawa daga karkashin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.