Isa ga babban shafi
Venezuela

Kasashen duniya sun mayar da martani kan zaben Venezuela

Akalla mutane 10 sun rasa rayukansu a wata sabuwar tarzoma da ta barke a Venezuela bayan gwamnati ta gudanar da zaben wakilan sake-rubuta kundin tsarin mulkin kasar, in da shugaba Nicolas Maduro ya yi ikirarin samun nasara. Kasashen duniya sun caccaki zaben, yayin da kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana damuwarta kan makomar Demokradiya a kasar.

'Yan adawa sun datse hanyoyi a yayin gudanar da zaben wakilan sake rubuta kundin tsarin mulki a Venezuela
'Yan adawa sun datse hanyoyi a yayin gudanar da zaben wakilan sake rubuta kundin tsarin mulki a Venezuela Reuters/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Kungiyar Tarayyar Turai, ta ce, bisa dukkan alamu, ba za ta amince da ingancin zaben wakilan sake- rubuta kundin tsarin mulkin kasar ba, da shugaba Nicolas Maduro ya yi ikirarin samun nasara bayan ya yi gaban kansa wajen gudanar da shi duk da gargadin da kasashen duniya suka yi ma sa.

An gudanar da zaben ne a yayin da kasar ke fama da rikicin siyasa da ya yi sanadiyar mutuwar jumullar mutane 120 a cikin watanni hudu.

Kungiyar kasashen Turai ta ce, zaben wanda aka gudanar a cikin irin wannan yanayi na tashin hankali, ba zai zama hanyar magance matsalolin kasar ba.

‘Yan adawan Venezuela sun lashi takobin gudanar da gagarumar zanga-zangar game gari da nufin karfafa matsayinsu na yin alla-wadai ta matakin murkushe su.

Amurka ta yi barazanar sanya wa Venezuela sabbin takunkumai saboda matakin gudanar da zaben da ta dauka.

A lokacin gudanar da zaben a jiya Lahadi, masu zanga-zanga sun kai hari a rumfunan zabe tare da rufe hanyoyi a sassa daban daban na kasar, lamarin da ya tinzira jami’an tsaro har suka bude mu su wuta.

Duk da wannan tashin hankali, hukumar zaben kasar ta ce, fiye da mutane miliyan takwas ne suka fito don kada kuri’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.