Isa ga babban shafi
Amurka

Stevie Wonder zai jagoranci bikin mawaka na yaki da yunwa

Wasu Fitattun mawakan duniya da suka hada da Stevie Wonder za su taka rawa wajen wani kasaitaccen bikin kaddamar da gidauniya domin yaki da talauci da kuma taimakawa yankunan da ake fama da yunwa, sakamakon zabtare tallafin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi.

Stevie Wonder mawakin Amurka
Stevie Wonder mawakin Amurka REUTERS/Jason Reed
Talla

Za a yi bikin ne a birnin New York na Amurka a ranar 23 ga watan Satumba

Masu shirya wannan gagarumin biki sun bayyana cewar cikin wadanda za su halarci taron har da Stevie Wonder da Pharell Williams.

Stevie Wonder ya ce bikin ya zo a wami lokaci da suka sadaukar da rayukansu domin kare al’umma da kuma nuna musu kauna.

An fara bikin ne da ake gudanarwa duk shekara tun shekarar 2012 wanda kan taimaka wajen matsin lamba ga shugabannin kasashen duniya wajen tabbatar da cewar sun sauke nauyin da ke kansu a taron Majalisar Dinkin Duniya.

Taron na bana na zuwa ne lokacin da yakin da ake fama da shi a Syria da Yemen ke ci gaba da haifar da matsala da kuma yunwar da aka samu a wasu kasashen Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.