Isa ga babban shafi
Amurka

Sabon daftarin dokar rage shigar baki a Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi bayan daftarin da wasu sanatoci biyu suka gabatar da ke neman a rage adadin bakin da ke shiga kasar da 50 %.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Daftarin na fatan ganin an rage adadin baki da ke shiga Amurka ne da akalla dubu 50 a cikin shekaru 10 masu zuwa, tare da rage yawan kason da ake bai wa ‘yan gudun hijira da ke shiga kasar.

 

Sai dai ‘yan majalisa daga bangaren Democrat na adawa da yunkurin, inda Anthony Blanken, tsohon mataimakin sakataren waje a mulkin Obama, ya ce dokar ta yi hannun riga da manufofi da matsayin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.