Isa ga babban shafi
Japan

Japan na bukin cika shekaru 72 da harin makamin Nukiliya na Hiroshima

Yau Lahadi  kasar Japan ke bukin cika shekaru 72 bayan da aka kai mata hari da makamin nukiliya a Hiroshima na farko da wannan shu'umin makami a duniya.

Wajen da ake bukin tuna harin nukiliya na Hiroshima yau lahadi.
Wajen da ake bukin tuna harin nukiliya na Hiroshima yau lahadi. RFI
Talla

Bukin na zuwa ne bayan da cikin watan jiya kasar ta Japan ta bi sahun wasu manyan kasashen duniya da suka mallaki makamin wato Birtaniya, Faransa da Amurka da suka yi watsi da wani kudiri na MDD dake hana wata kasa a duniya mallakan makamin.

Kasar Japan  ta kasance ita kadai ta taba fuskantar bala’in makamin nukiya a fadin duniya wanda aka kai mata cikin shekara ta 1945.

Da yake jawabi Firaministan kasar Shinzo Abe a bukin tuna ranar ya bayyana burin kasar na ganin babu wata kasa a duniya da aka bari ta mallaki wannan makami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.