rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gabas ta Tsakiya Afghanistan Saudiya Syria Daular Larabawa Somalia Sudan Pakistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kisan kai ya lakume rayuka fiye da yaki a Gabas ta Tsakiya

media
Kisan kai na barazana ga wanzuwar kananan yara da matasa a yankin Gabas ta Tsakiya kamar yadda rahoton binciken ya nuna REUTERS/Omar Sobhani

Wani rahoton bincike ya nuna cewa, adadin mutanen da ke rasa rayukansu ta hanyar kisan kai ya ninka adadin mutanen da ke mutuwa a yakin da ake fama da shi a gabas ta tsakiya da yankuna makwabta.


Rahoton da Mujallar Kula da Lafiyar Jama’a ta duniya ta fitar , ya ce kimanin mutane miliyan 14 da dubu 400 ne suka rasa rayukansu a shekarar 2015 sanadiyar kisan kai a yankin gabashin tekun Mediterranean da suka hada da kasashe 22 kamar Afghanistan da Iran da Saudi Arabia da Pakistan da Somalia da Sudan da Syria da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

Yake-yake a yankin mai kunshe da mutane miliyan 600 ya lakuma rayuka dubu 144 a shekarar ta 2015, abin da ke nuna cewa, wadanda suka mutu ta hanyar kisan kan sun zarce wadanda suka mutu a yaki da ninki 10.

Ali Mokdad, darekta a cibiyar dabbaka yankin gabas ta tsakiya da ke jami’ar Washington ta Amurka, ya ce matsalar kisan kai na barazana ga wanzuwar kananan yara da matasa a yankin.

Mr. Mokhad ya ce, makomar wannan yanki na cikin barazana har sai an samar da hanyoyin wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

Masu binciken sun kuma gano cewa, an samu karuwar mutanen da ke shiga damuwa ta zuci a yankin na gabashin Mediterranean, lamarin da ke sanya wasu daukan rayukansu da kansu ko kuma kashe wasu daban.