Isa ga babban shafi
MDD

''Najeriya da Somalia da Sudan ta Kudu da Yemen na kukan Yunwa''

Majalisar Dinkin Duniya ta sake gargadin cewar yanzu haka akalla Mutum miliyan 20 ke fuskantar barazanar Ukubar yunwa sakamakon yaki a kasashen Najeriya da Somalia da Sudan ta kudu da kuma Yemen.

Wasu daga cikin 'Yan gudun hijiran Najeriya da ke bukatar taimako
Wasu daga cikin 'Yan gudun hijiran Najeriya da ke bukatar taimako Reinnier KAZE / AFP
Talla

Kwamitin Sulhu na Majalisar ya bayyana damuwa kan kuncin da wadanan mutane ke ciki, musamman abinda ya shafi tallafin gaggawa da kuma magance matsalar baki daya.

Jami’in jinkai na Majalisar ya ce Dala biliyan 2 da rabi kawai aka samu daga gidauniyar kusan Dala biliyan 5 da aka kaddamar domin taimakawa wadanan kasashe.

A cewar Majalisar rashin bada taimako a kan lokaci na iya barazana ga rayuwa miliyoyin mabukatan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.