Isa ga babban shafi
MDD

ISIS na ci gaba da kitsa kai hare-hare kasashen duniya

Wani Rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya ce har yanzu kungiyar ISIS na ci gaba da kitsa hare-haren da ake kai wa kasashen duniya duk da nasarar da aka samu kan Cibiyoyin su da ke Syria da Iraqi.

kungiyar ISIS na ci gaba da kitsa hare-haren da ake kai wa kasashen duniya
kungiyar ISIS na ci gaba da kitsa hare-haren da ake kai wa kasashen duniya REUTERS/Stringer/Files
Talla

Rahotan mai shafi 24 da masana harkar tsaro suka rubutawa kwamitin Sulhu ya ce ana samun wahala wajen gane kudaden da mutane ke aikawa kungiyar a matsayin tallafi.

Rahotan ya ce kungiyar na fadada karfin ta zuwa kudu maso Gabashin Asiya, musamman kudancin Philippines inda yanzu haka aka kashe mutane kusan 700.

Masanan sun bukaci sa ido kan yara da matasa wadanda ake yaudarar su domin sanya su cikin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.