rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Lafiya Belgium Holland Jamus Hong Kong

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gurbataccen Kwai ya fara isa Asiya daga Turai

media
Badakalar gurbataccen kwan ta haddasa taya da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen Turai Reuters

Badakalar yaduwar gurbataccen kwai da ta mamaye kasashen Turai 15, ta fara shafar nahiyar Asia, in da a baya-bayan nan matsalar ta isa Hong Kong.


Ministocin kasashen Turai da manyan jami’an kula da lafiyar abinci, za su gudanar da taro a ranar 26 ga watan Satumba, a wani yunkuri na kawo karshen zarge-zargen da kasashen nahiyar ke yi wa juna dangane da yaduwar kwan.

Matsalar dai ta haifar da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Belgium da Netherland da Jamus, da suka kasance kan gaba a jerin kasashen da matsalar ta fi shafa.