Isa ga babban shafi
Colombia

An kawo karshen yaki shekaru 50 a Colombia

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos ya bayyana cewa, rikicin mayakan FARC da kasar ta yi fama da shi a tsawon shekaru 50, ya kawo karshe baki daya.

An kawo karshen yakin Colombia na shekaru 50
An kawo karshen yakin Colombia na shekaru 50 LUIS ROBAYO / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da aka karbe dukkanin muggan makaman da ke karkashin ikon mayakan na FARC.

Shugaba Santos ya tabbatar da haka ne a yayin da ya bame wata katuwar mota makare da makaman da aka karbe daga hannun mayakan, in da aka yi awon gaba da motar zuwa wani sansanin da ke yankin arewacin kasar.

A wannan sansanin ne za a cimma wata yarjejeniya a hukmace karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da zimmar sasantawar karshe tsakanin mayakan da gwamnati.

Santos ya ce, daga yanzu an bude sabon babin rayuwa a Colombia.

Wannan dai wani tarihi ne mai matukar muhimmaci da a aka kafa a kasar kamar yadda Santos ya fadi.

Shugaban ya ce, Colombia ta shafe tsawon shekaru 198 a matsayin Jamhuriya, kuma ba ta taba samun tashin hankali ba kamar rikicin FRAC, amma a yanzu, zancen ya zama tarhi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.