Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya fito ya soki masu yada kyamar jinsi

Bayan Sukar da ya sha daga sassa daban-daban na Amurka, shugaba Donald Trump ya fito karara ya soki masu yada kyamar jinsi a cikin kasar.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya soki nuna wariyar jinsi
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya soki nuna wariyar jinsi REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A jawabinsa zuwa ga Amurkawa ta kafar talabijin, Donald Trump ya bayyana nuna ban-bancin launin fata a matsayin abin kyama, kana ya ce duk mai yada wannan mai laifi ne.

Ya bayyana halayen kungiyoyi irin su KKK da ‘yan ra’ayin Nazi da kuma fararen fata masu wariyar jinsi a matsayin abinda ya sabawa matsayin Amurka.

Trump ya ce suna Alla-wadai da nuna kyama da tashin hankalin da wadannan kungiyoyi ke haifar wa.

Wadannan kalamai na shugaban na zuwa ne kwana guda, bayan mummunar sukar da ya fuskanta kan kin nuna ba-cin ran sa da rawar da kungiyar fararan fata masu nuna kyama ta taka, wanda ya kai ga kashe Hether Hayer tare da wasu jami’an ‘Yan Sanda biyu da suka yi hadarin jirgin sama a Virginia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.