rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Faransa Jamus Rasha Birtaniya Sweden ISIL Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen duniya sun yi tir da harin Barcelona

media
Jami'an 'yan sanda sun kai dauki bayan harin Barcelona na Spain da ya hallaka mutane 13 REUTERS/Sergio Perez

Shugabannin Kasashen duniya na ci gaba da aikewa da sakwannin jaje ga gwamnatin Spain kan harin ta’addancin da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaiwa a birnin Barcelona, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 baya ga 100 da suka jikkata.


Rahotanni sun kuma ce, wasu mutane 7 sun jikkata lokacin da wasu 'yan ta’adda suka kai hari a Cambrils mai tazaar kilomita 120 daga Barcelona a yau juma’a, amma an harbe maharan guda 5 har lahira.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya bukaci kasashen duniya da su zage dantse a yaki da ta’addanci, yayin da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ya ce, suna tare da Spain 100 bisa 100.

Ita ma, shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi alla-wadai da harin na Barcelona, in da ta jajanata wa mutanen Spain.

Tuni dai aka cafke wasu da ake zargi da hannu a harin kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

An dai kai harin ne a unguwar Las Ramblas mai cike da hada-hadar jama’a musamman bakin masu yawon bude ido .

Ba a karon farko kenan ba da ‘yan ta’adda ke amfani da motoci wajen kai hari a kasashen Turai.

Sannan kuma 'yan ta'adda sun kai hare-hare da dama a kasashen na Turai a cikin wannan shekarar.

A ranar 3 ga watan Agusta, wasu mahara 3 sun kai hari a gadar London, in da  suka daba wa mutane wuka, tare da hallaka mutane 8 da raunana 48.

A ranar 22 ga watan Mayu, wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 22 da raunana 59 a wajen bikin rawar da aka shirya a Manchester na Ingila.

A ranar 7 ga watan Afrilu, wani ya tuka motar daukar kaya cikin kasuwa a Stockholm na Sweden, in da ya kashe mutane 5 ya kuma raunana 15.

A ranar 22 ga watan Maris, wani ya daba wa dan sanda wuka a kusa da Majalisar Birtaniya, bayan wata mota ta afka wa matafiya a gefen hanya kusa da Westminster. Mutane 6 suka mutu, 20 kuma suka jikkata.