Kawo karshen masu safarar hodar ibilis a Philippines
Yan sandan kasar Philippines sun halaka wasu mutane 13 bisa samunsu da laifin tu’ammuli da miyagun kwayoyi, lamarin da ya kara yawan wadanda ‘yan sandan suka halaka zuwa 80 a cikin mako guda.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Rodrigo Duterte ya bada umarnin matsa kaimi wajen kawo karshen miyagun kwayoyi a kasar.
A farkon makon da muke ciki, akalla masu tu’ammulin da miyagun kwayoyi 67 ‘yan sandan kasar ta Philippines suka bindige, yayinda da suka kame wasu 200 a babban birnin kasar Manilam da sauran lardunan kasar.
Matakin da mataimakiyar shugaban kasar ta Philippines Leni Robredo ta yi Ala wadai da shi, a matsayin take hakkin bil adam.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu