Alhazzai miliyan 2 na tsayuwar Arfah
Sama da Mahajjata miliyan 2 daga sassan duniya da ke aikin hajji a Saudiya ke tsayuwar Arfah a yau Alhamis, wanda shi ne rukuni mai girma cikin rukunan aikin hajji.
Wallafawa ranar:
Mahajjata na soma tsayuwar ne daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, kuma suna gudanar da ayyuka na Ibadah da suka hada da yin addu’oi a filin na Arafah.
A Tsayuwar Arfa ba ana nufin mutum ya tsaya ba hutawa tun safe har faduwar rana ba, ana so ne mutum ya kasance a cikin filin Arfah har zuwa faduwar rana.
Bayan hawan Arfa ne washegari al’ummar musulmi a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan Sallar layya da aka fi sani da sallah Babba a kasar Hausa.
Taron aikin Hajji shi ne taron mutane mafi girma a duniya duk shekara.
Aikin Hajji yana cikin Shika-shikan Musulunci guda biyar da aka wajabta wa Musulmi ya gudanar akalla sau daya a rayuwar shi idan har yana da wadata kuma yana cikin koshin lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu