Rasha da Faransa sun yi gargadi kan Korea Ta Arewa
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gargadi yiwuwar samun gagarumin tashin hankali a tsibirin Koriya ta Arewa, yayin da a bangare guda Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean Yves Le Drien ya gargadi yiwuwar rikicin ya shafi nahiyar Turai.
Wallafawa ranar:
A ranar Talatar da ta gabata ne, Korea ta Arewa ta harba makami mai linzami ta sararin samaniyar Japan zuwa tekun Pacific, abin da ya karfafa fargaba game da shirinta na makamin Nukilya.
Gwajen-gwajen Koriya Ta Arewa sun haifar da cacar-baka tsakaninta da Amurka, yayin da Majalisar Dinkin Duyniya ta kakaba wa kasar takunkumai.
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce, zaman tattaunawar keke da keke ne kawai zai kawo karshen wannan takardama
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu