Isa ga babban shafi
Myanmar

Musulman Rohingya dubu 60 sun nemi mafaka a Bangladesh

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akalla Musulman Rohingya dubu 60 ne suka tsere zuwa Bangladesh a cikin kwanaki takwas sakamakon rikicin da ake fama da shi a jihar Rakhine da ke Myanmar.

Wasu 'yan Rohingya da ke neman mfaka a Bangladesh
Wasu 'yan Rohingya da ke neman mfaka a Bangladesh REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Vivian Tan ta shaida wa kamfanin Dillancin labaran Faransa na AFP cewa, akwai yiwuwar adadin Musulman da ke neman mafaka a Bangladesh ya karu nan gaba.

Tuni dai Hukumar bada tallafin abinci ta duniya ta dakatar da bada tallafin abincin ga jihar ta Rakhine mai fama da rikicin.

Ana zargin 'yan tawayen Rohingya da haddasa rikicin na baya-bayan nan sakamakon harin da suka kai kan jami'an tsaro a ranar 25 ga wata Agustan da ya gabata.

Rahotanni na cewa, kimanin mutane 400 da suka hada da fararen hula suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.