Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya ziyarci wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

Shugaban Amurka Donald Trump na ziyararsa ta biyu a jihohin Texas da Louisiana don ganawa da wadanda ibtila’in guguwar Harvey da ambaliyar ruwa suka shafa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara isa Houston na Texas don ganawa da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
Shugaban Amurka Donald Trump ya fara isa Houston na Texas don ganawa da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa Reuters
Talla

Kimanin mako guda kenan da guguwar ta haddasa ambaliyar ruwan, wadda ta shafi sassa da dama na Texas da Louisiana, yayin da aka alakanta mutuwar mutane 43 da ibtila'in, wanda ya raba kimanin dubu 43 da muhallansu.

Shugaba Trump dai ya bukaci Majalisar kasar da ta bada umarnin sakin Dala biliyan 7. 8 don tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.

Sai dai a cewar Gwamnan Texas, Greg Abbott, suna bukatar sama da Dala biliyan 125 a matsayin tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.