Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta yi watsi da bukatar saka wa Koriya takunkumi

Kasar Rasha ta yi watsi da duk wani yunkurin kakabawa Koriya ta Arewa sabbin takunkumi, yayin da Amurka ta yi wa Japan da Koriya ta kudu alkawarin samun sabbin makaman da za su kare kansu.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Reuters/路透社
Talla

Shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya yi watsi da shirin sanyawa Koriya ta Arewa Karin takunkumi, yayin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi kan daukar matakan soji akan kasar.

Duk da hadin kan kasashen duniya da aka samu wajen watsi da kuma yin allawadai ga gwajin makamin da Koriya ta yi, matsayin Rasha da China ya nuna rarrabuwar kawuna kan hanyoyin da ya dace abi wajen warware matsalar.

Amurka ta tauna tsakuwa da kuma barazanar katse duk wata hulda da Koriyar da China da Rasha sun bukaci shawo kan gwamnatin Koriya ta Arewar domin tattaunawa da ita.

Jakadan Koriya ta Arewa Han Tae Song ya bayyana gwajin makamin a matsayin matakin kare kai da kyauta ga Amurka, yana mai cewa Amurkan zata samu Karin kyaututtuka daga Koriyar muddin ta ci gaba da yi mata barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.