Isa ga babban shafi
Syria

Sojan Rasha Sun Kashe Fararen Hula 34 A Syria

Wasu hare-hare da sojan Rasha suka kai kasar Syria yau Lahadi ya yi sanadiyar kashe fararen hula akalla 34 a lokacin da suke tserewa daga yankin Deir Ezzor inda aka yi wa masu jihadi kofar rago saboda Dakarun Amurka da na Rasha suka sa su a tsakiya.

Wasu Sojan dake goyon bayan Shugaba Bashar al-Assad an duba ababan hawa a kasar.
Wasu Sojan dake goyon bayan Shugaba Bashar al-Assad an duba ababan hawa a kasar. Reuters/路透社
Talla

Wasu kungiyoyin dake sa idanu kan yakin na Syria na cewa ana ta samun gawarwakin mutane a yankin  Gunduman Deir Ezzor inda Rasha ta kai harin.

Majiyoyin na cewa cikin mamatan akwai kananan yara tara, sannan kuma akwai wasu da yawa da suka jikkata.

A watan tara na shekara ta 2015 ne kasar Rasha ta shiga cikin yakin a Syria domin taimakawa shugaba Bashar Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.