rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Barack Obama Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya gana da 'yan Democrat kan shirin DACA

media
Da dama daga cikin Amurkawa na adawa da matakin soke shirin DACA REUTERS/Kevin Lamarque

Manyan ‘yan Majalisun Jam’iyyar Democrat a Amurka sun ce sun samu fahimtar juna a tattaunawar da suka yi da shugaba Donald Trump kan dokar da ya soke wadda ke kare bakin da suka shiga Amurka suna kananan yara.


Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawar, Chuck Schumer da takwararsa a Majalisar Wakilai Nancy Pelosi sun ce, za su samar da dokar da za ta kare irin wadannan baki da kuma dokar kare iyakokin Amurka.

Sai dai bangarorin biyu ba su cimma matsaya ba kan shirin Trump na gina katanga tsakanin Amurka da Mexico.

Fadar shugaba Trump ta ce, shugaban zai ci gaba da janyo hankalin Majalisar domin samun goyan bayanta kan shirin gina katangar.

A farkon wannan watan ne, shugaba Trump ya sanar da matakin soke shirin da aka fi sani da DACA wanda gwamnatin Barack Obama ta samar don bai wa dubban kananan yara 'yan gudun hijira damar zama a Amuka duk da cewa ba su da takardun izinin zama.