Isa ga babban shafi

Catalonia ya kaddamar da shirin kuri'ar ballewa daga Spain

Yankin Cataonia ya kaddamar da shirin gudanar da kuri’ar raba gardama domin ballewa daga kasar Spain sakamakon goyan bayan da gwamnatin yankin ta bai wa shirin duk da adawar da gwamnatin Spain ke yi.

Wasu daga cikin al'ummar yankin Catalonia a Spain
Wasu daga cikin al'ummar yankin Catalonia a Spain PAU BARRENA / AFP
Talla

Daruruwan mazauna yankin sun yi wani gangami a wurin wasan hawan kaho a birnin Tarragona, in da suka rika shelar cewa, za su kada kuri’a lokacin da shugaban yankin, Carles Puigdemont ya isa domin neman goyan bayansu.

Tuni gwamnatin Spain ta yi barazanar kama Magadan Garin Yankin da kuma hana gudanar da zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.