rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Myanmar Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU ta yi tir da harin da ake kai wa mutanen Rohingya

media
Kasashen duniya na ci gaba da sukar kisan da ake yi wa 'yan kabilar Rohingya a Myanmar REUTERS/Darren Whiteside

Kungiyar Kasashen Turai ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa 'yan kabilar Rohingya, yayin da kungiyar Amnesty International ta gabatar da wasu hotunan da ta dauka ta tauraron dan Adam da ke nuna yadda sojoji ke kona kauyukan Rohingya.


Shugaban kungiyar kasashen Turai Jean-Claude Juncker ya bayyana kaduwarsa kan rikicin wanda ya bayyna a matsayin wani yunkurin shafe daukacin wata kabila daga doron kasa.

Juncker ya ce, Kungiyar Kasashen Turai za ta dauki mataki tare da kasashen da ke makwabtaka da Myanmar domin taimaka wa Rohingya.

Ita kuwa kungiyar Amnesty cewa ta yi ta dauki wasu hotuna ta tauraron dan Adam da ke nuna yadda sojojin Myanmar ke bi suna kona kauyukan 'yan kabilar Rohingya.

Kungiyar ta ce, akalla kauyuka 26 aka kona, in da ta gabatar da hotunan wutar da ke ci a wurare 80.

Olof Blomqvist, jami’in kungiyar ya ce, yanzu haka akasarin Jihar Rakhine na ci da wuta.

Shi ma Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana hare-haren da ake kai wa Rohingya a matsayin abin da ba za’a amince da shi ba.