rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane sun jikkata a wata fashewa a London

media
Jami'an tsaron Birtaniya na bincike kan fashewar da aka samu a layin dogo na karkashin kasa da birnin London REUTERS/Kevin Coombs

Jami’an ‘yan sandan birnin London na gudanar da bincike kan wata fashewa da aka samu a layin dogo na karkashin kasa da ke dandalin Parsons, in da mutane da dama suka samu rauni.


‘Yan sandan na kallon lamarin da ta’addaci, yayin da mutane da dama suka samu raunin na kunar wuta a fuskokinsu, in da wasu kuma suka jikkata saboda tirmitsitsi.

Jami’an tsaron da ke yaki da ta’addanci ne ke jagorantar gudanar da bincike kan lamarin.

Kamfanin Dillancin Labrai na Reuters ya rawaito cewa, motocin daukan marasa lafiya da injinan kashe wuta da jirage masu saukar ungulu sun isa tashar layin dogon.

Firaministar Birtaniya Theresa May ta ce, tana tare da wadanda suka jikkata da kuma jamian agajin gaggawa da suka kai dauki.

Magajin garin birnin London, Sadiq Khan ya bukaci jama’a da su kwantar da hankukansu, in da ya ce, babu wata barazanar ta’addanci da za ta tsorata su.