Trump ya yi jawabin farko ga zauren Majalisar Dinkin Duniya
A Jawabinsa na farko ga zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, shugaban Amurka Donald Trump, ya ce, Majalisar ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Wallafawa ranar:
Trump ya bukaci Majalisar da ta mayar da hankali kan ci gaban al’umma tare da kawo karshen bin tsarin-daki-daki da take yi, wanda ya yayi gargadin cewa yana haifar da tarnaki ga tafiyar da ayyuakan Majalisar.
A nashi bangaren Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres ya mayar da martani kan kalaman Donald Trump, da cewa ya samar da sauyi a tsarin ayyuka na ci gaba ta hanyar dukufa wajen mun taimakawa kasashen duniya cimma muradun ci gaba nan da shekarar 2030.
Zalika a tuni Majalisar ta fara kokarin saukaka bin tsarin daki-daki da kuma raba karfin iko kuma a zahirance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu