Isa ga babban shafi
Amurka

Za mu ga bayan Koriya ta Arewa- Trump

A yayin gabatar da jawabinsa na farko a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a wannan Talata, shugaban Amurka Donald Trump ya ce, kasarsa za ta ga bayan Koriya Ta Arewa da ke gwaje-gwajen makamin Nukiliya.

Shugaban Amurka Donald Trump a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Amurka Donald Trump a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Trump ya ce, Amurka na da karfi da hakuri, amma matukar aka kai ta bango don kare kanta da kawayenta, to lallai ba su da wani zabi illa ganin bayan Koriya ta Arewa.

Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba jerin takunkuman karayar tattalin arziki kan Koriya ta Arewa bisa gwaje-gwajenta na makamin Nukiliya, abin da ya janyo ma ta suka daga kasashen duniya.

A bangare gida, shugaban na Amurka ya jaddada matsayinsa na adawa da yarjejeniyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya kan shirinta na Nukiliya.

An dai cimma yarjejeniyar ce a lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama, yayin da Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin abin kunya.

Trump ya soki gwamnatin Iran wadda ya bayyana a matsayin mai mulkin kama-karya da ke da burin durkusar da yankin gabas ta tsakiya.

Trump ya kuma yi tsokaci game da rikikcin Venezuela , in da ya ce, Amurka ba za ta amince da wannan matsalar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.