Isa ga babban shafi
Faransa

Mace mafi kudi a duniya ta rasu

Fitacciyar ‘yar kasuwar nan ta kasar Faransa Liliane Bettencourt kuma ta 14 a jerin masu kudin duniya ta mutu tana da shekaru 94 a duniya. Kafin rasuwar Bettencourt dai ita ce mafi girman hannun jari a shahararren kamfanin kayan kwalliyar nan na L’Oreal.

Liliane Bettencourt dai yanzu haka ita ce ta 14 a jerin masu kudin duniya yayin da kuma ita ce ta daya a mata da ta fi kowacce mace kudi a duniya baki daya.
Liliane Bettencourt dai yanzu haka ita ce ta 14 a jerin masu kudin duniya yayin da kuma ita ce ta daya a mata da ta fi kowacce mace kudi a duniya baki daya. Reuters
Talla

Tun a shekarar 2011 ne Liliane ta fara fuskantar matsaloli wajen gudanar da harkokin kasuwancin ta da kanta, yayin da ta ajje aikin ta da kamfanin na L’Oreal a shekarar 2012.

Kuma tun daga wannan lokaci ne aka rabu da ganin Liliane a cikin al’umma baya da likitoci suka tabbatar da tana fama da cutar kidimewar kwalkwalwar tun a shekarar 2006, sakamakon yawan shekarunta.

Liliane dai ta taka muhimmiyar rawa wajen bai wa tsohon shugaban Faransa Nicholas Sarkozy gudunmawar kudi don gudanar da takarar zabe.

Bayanai na nuni da cewa Liliane ta fara shigowa ana damawa da ita cikin harkokin kasuwanci tun tana da shekaru 15 a duniya, bayan data rasa mahaifiyarta tun tana da shekaru 5.

An dai haifi Bettencourt a ranar 21 ga watan Oktoban shekarar 1922 a birnin Paris na Faransa.

Rahotanni sun ce mahaifin dan kasuwa ne kuma shi ne ya samar da wani nau’in sinadarin rina gashi a shekarar 1907, bayan habakar kasuwancin kuma ya bude kamfanin kayan kwalliya da ya sanyawa suna Aureala yayin da daga bisani aka sauya masa suna zuwa L’Oreal a shekarar 1939.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.