Isa ga babban shafi
Iran

Iran Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami

Kasar Iran ta yi gwajin wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango, duk da cewa  Amurka na ta jan kunnenta da cewa muddin ta sami hujja yarjejeniyar da aka kulla da ita zai sukurkuce.

Makamin da Kasar Iran ta yi gwaji 2017
Makamin da Kasar Iran ta yi gwaji 2017 President.ir/Handout via REUTERS
Talla

Tashan Talabijin na kasar ya sanar da cewa gwajin na makamin mai suna Khoramshahr an yi nasara, yayin wani  fareti na Soja a birnin Tehran.

Makamin wanda ke dauke da bidiyo a cikin sa na  iya tafiya mai nisan kilomita 2,000.

Ministan Tsaro na kasar ta Iran Amir Hatami ya bayyana cewa muddin wasu na maganganu dake barazana dole a kara karfafa harkan tsaron kasa, kuma babu yadda kasar za ta jira wani izini kafin yin duk wani makami da take so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.