Isa ga babban shafi
India

Yara na fuskantar cin zarafi a duniya

Wani Bincike ya bayyana cewar kusan yara uku daga cikin hudu a duniya na fuskantar wani nau’in tashin hankalin da ya kunshi fada a makaranta ko cin zarafi ko kuma kisan kai wanda ke matukar illa ga rayuwa da kuma tattalin arziki.

'Yan gudun hijirar Najeriya a sansanin Dar es Salaam da ke tafkin Chadi
'Yan gudun hijirar Najeriya a sansanin Dar es Salaam da ke tafkin Chadi LA Bagnetto
Talla

Binciken wanda wata kungiyar da ke da Cibiya a India da ake kira ‘Know Violence in Childhood’ ta gudanar ya bayyana cewar akalla yara sama da biliyan daya da rabi da suka kunshi maza da mata a duniya ke fuskantar kuncin rayuwa da kuma cin zarafi a shekara, kuma matsalar inji rahotan, ta fi kamari ne a nahiyar Afirka.

Shiva Kumar, daya daga cikin wadanda suka jagoranci binciken ya ce irin wannan cin zarafi yana lalata yara da iyalai da kuma al’umma a kasashen da suka ci gaba da kuma kasashe matalauta.

Rahotan ya bayyana azabtarwa da ake samu a gida a matsayin cin zarafin da aka fi samu, wanda ya kan shafi yara akalla biliyan guda da miliyan 300 da ke da shekaru kasa da 14, yayin da fada a makaranta ke shafar yara miliyan 138 da ke da shekaru 13 da kuma miliyan 123 wadanda ke da shekaru 15.

Kumar ya ce alkalumman binciken sun nuna cewar yara mata miliyan 18 da ke da shekaru 15 zuwa 19 ke fuskantar matsalar fyade.

Har ila yau wannan rahoto ya bayyana cewar matsalar fyaden ta fi kamari a Afirka inda kashi sama da 10 na yara mata masu shekaru 15 zuwa 19 suka fuskanci matsalar a rayuwarsu.

Rahotan yace yaran da suka fuskanci irin wannan matsala basa taba mantawa a rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.