Isa ga babban shafi
Myanmar

MDD ta dage kai ziyara yankin mutanen Rohingya

Matsalar yanayi ta tilastawa Majalisar Dinkin Duniya dage ziyarar da ta shirya a karon farko zuwa jihar Rakhine a Myanmar mai fama da rikici wanda ya tursasawa ‘yan kabilar Rohingya musulmi yin kaura.

'Yan gudun hijirar Rohingya
'Yan gudun hijirar Rohingya REUTERS/Cathal McNaughton
Talla

Adadin musulmi ‘yan kabilar Rohingya da suka tsere zuwa Bangaladesh ya kai kimanin dubu 500 yanzu haka, kuma hukumomin Myanmar sun amince kungiyoyin agaji na kasa da kasa shigowa don tallafawa wadanda rikicin ya shafa.

Wannan ne karon farko da hukumomin kasar suka amince a shiga jihar ta Rakhine tun bayan barkewar rikicin a watan Agusta.

A baya dai hukumomin kasar sun tilastawa kungiyoyin agaji na kasa da kasa ficewa daga jihar ta Rakhine lamarin da ya sa majalisar dinkin duniya nuna damuwa tare da bukatar izinin shigar jami’an agaji da na jinkai kasar don tallafawa wadanda rikicin ya shafa.

Ziyarar wadda ita ce irinta ta farko ta tanadi kayan agaji na mutune sama da dubu dari bakwai.

Kungiyoyin agajin dai sun bayyana cewa dubban ‘yan kabilar Rohingya da suka rage a jihar ta Rakhine na cikin tsananin bukatar abinci da magunguna da matsugunai bayan shafe wata guda karkashin gallazawar jami’an soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.