Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gabatar da sabon shirin sa na zabtare haraji

Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da sabon shirin sa na zabtare haraji ga manyan kamfanoni da kuma soke haraji daga dukiyar da aka gada domin bunkasa tattalin arzikin kasa.

Shugaba Donald Trump a lokacin gabatar da sabon shirin zabtare haraji a Amurka
Shugaba Donald Trump a lokacin gabatar da sabon shirin zabtare haraji a Amurka REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shirin ya nuna cewar za a ragewa kamfanoni kudaden da suke biya daga kashi 35 zuwa kashi 20.

Shugaba Trump ya bayyana shirin da ake amfani da shi da ya gada a matsayin wanda ya hana samun ci gaban tattalin arziki, inda ya bayyana na sa a matsayin gagarumin shirin Jam’iyyar Republican.

Trump ya kuma bayyana shirin a matsayin wani juyin-juya halin da zai amfanar da matsakaitan ma’aikata a dai-dai lokacin da ake samun karuwar kamfanonin da suke kwarara zuwa Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.