rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa zata taka rawa domin magance rikicin Iraqi

media
Hukumomin Bagdaza REUTERS/Alaa Al-Marjani

Bisa gayyatar Shugaban Faransa Firaministan Iraki Haider Al Abadi zai kai wata ziyara Faransa ranar 5 ga watan gobe, Shugabanin biyu Emmanuel Macron da Al Habadi za su gana domin tattance hanyoyin da suka dace domin dakile duk wata barrazana da kan iya kawo cikas ga kokarin hukumomin Iraki na sake dawowa da doka da oda a sasan kasar.


Kasar Iraqi ta bada umarni dakatar da sauka da tashin jiragen sama a birnin Arbil na yankin Kurdawa, wanda ke a matsayin martani ga zaben raba gardamar balewa daga kasar da kurdawan suka kada.

Hukumomin Bagadaza sun ce zasu ci gaba da matsin lambar tabbatar da cewa kurdawan su mika kai.

Wannan mataki daga hukumomin Bagdaza na a matsayin barrazana ga tattalin arzikin yankin a cewar kakakin ministan sufuri na yankin Kurdawa Oumed Mohamas.