rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya ‘Yan gudun Hijira Amurka Tarayyar Turai Myanmar Sudan ta Kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane miliyan 2 na gudun hijira a sassan duniya

media
Mutane da dama na tsallaka teku don neman mafaka a kasashen Turai. Angelos Tzortzinis / AFP

Wani sabon rahoto da Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na cewa, sama da ‘yan gudun hijira miliyan biyu ke guje wa yake-yake a sassan duniya, in da wasu daga cikinsu ke fuskantar cikas a kasashen Turai da Amurka.


Kwamishinan Kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Duniya Duniya, Filippo Grandi ya ce, akwai ‘yan gudun hijira dubu 650 daga kasar Sudan ta Kudu, sai wasu dubu 500 Musulmi ‘yan kabilar Rohingya na Myanmar wadanda ala tilas suka guje wa gidajensu zuwa Bangladesh saboda yddaa ake azabtar da su.

Grandi ya shaida wa taron mako guda a Geneva cewa, a wannan shekara da muke ciki kawai sama da mutane miliyan 2 suka shiga halin kunci saboda guje wa wuraren da suke zaune don neman mafaka a wasu wuraren.

Grandi ya kara da cewa, mafi yawa kan isa wuraren da suka sami mafakan ne a tagayyare cikin rashin kosasshiyar lafiya ga kuma yunwa, yayin da wasu yaran aka raba su da iyayensu.

A cewar Kwamishinan ‘yan gudun hijirar, ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, ‘yan gudun hijira miliyan 17 da dori ke karkashin kulawar hukumar, amma daga bisani sun ragu domin wasu sun koma kasashen da sukla fito.