Isa ga babban shafi
Duniya

China za ta jagoranci amfani da sabbin hanyoyin samun makamashi a Duniya

HUKUMAR Kula da makamashi ta duniya ta kara yawan hasashen da ta yi na samun habakar makamashin da bai da nasaba da gas ko kwal nan da shekaru 5 masu zuwa sakamakon nasarar da aka samu a shekarar 2016.

A cewar hukumar ana sa ran China ta jagorancin amfani da sabbin hanyoyin samun makamashin yayinda Amurka da Indiya za su mara mata baya.
A cewar hukumar ana sa ran China ta jagorancin amfani da sabbin hanyoyin samun makamashin yayinda Amurka da Indiya za su mara mata baya. Reuters
Talla

Yayin gabatar da rahotan ta na tsakiyar shekara, Hukumar ta bayyana fatar ta na ganin an samu karuwar samun hasken wutar lantarki ta sabbin dabarun zamani da zai kai gigawatts 920 a fadin duniya, wanda ya nuna karuwar kashi 43 kafin shekara ta 2022 saboda yadda ake samun goyan bayan shirin watsi da hanyar gas da kwal domin rungumar hanyoyin hasken rana da iska.

A shekarar 2016 an samu karuwar haske lantarkin da ake samarwa a duniya da ya kai gigawatts 165, wato Karin kashi 6 kan yadda aka samu a shekarar 2015 ta hanyoyin hasken rana da iska da kuma kashin dabbobi da tsirai.

Rahotan hukumar ya ce ta hanyar rana ko solar kawai, an samu karuwar gigawatts 74 bara, wanda shine irin sa na farko.

Hukumar ta ce China ita ce kasar ta za ta yi jagorancin amfani da sabbin hanyoyin samun makamashin, sai kuma Amurka, yayin da ake saran India ta zarce kungiyar kasashen Turai nan da shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.