rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Spain na zanga-zangar ballewar Catalonia

media
Jama'ar yankin Catalonia da ke neman ballewa daga Spain REUTERS/Susana Vera

Al’ummar Spain na shirin gudanar da gagarumar zanga-zangar adawa da neman ‘yancin yankin Catalonia wanda ce, ya samu kashi 90 na masu kada kuri’a da ke goyon bayan ballewa daga kasar.


Ana saran gudanar da gangamin a Madrid da sauran manyan birane da ke kasar.

Wannan na zuwa ne bayan a karon farko gwamnatin Spain ta bada hakuri ga mutanen yankin Catalonia da jami’an ‘yan sandanta suka jikkata a lokacin kuri’ar raba gardamar da gwamnatin ke kallo a matsayin haramtacciya.

Shugabannin yankin na Catalonia sun yi barazanar yin gaban kansu wajen ayyana yankin a matsayin mai cin gashin kai, yayin da Firaministan spain, Mariano Rajoy ya lashi takobin dakatar da wannan yunkuri.

Da farko dai bangarorin biyu sun nuna alamun sasantawa da juna don magance rikicin siyasar kasar da ka iya jefa yankin Turai cikin wani hali.