Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ba ta da shirin haramta makamin nukiliya

Amurka ta ce, ba ta da niyyar sanya hannu kan yarjejeniyar haramta mallakar makamin nukiliya wadda ta samu goyon bayan kasashen duniya 122 a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Kasashen duniya na fargabar irin ta'adin da makamin nukiliya zai iya yi a duniya
Kasashen duniya na fargabar irin ta'adin da makamin nukiliya zai iya yi a duniya REUTERS/Grigory Dukor
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kyautar Nobel da aka bai wa kungiyar ICAN da ke fafutukar kawo karshen amfani da makamin nukiliya a duniya.

A cewar Amurka, yarjejeniyar ba za ta taka wata muhimmiyar rawa ba wajen tabbatar da zaman lafiya ko kuma inganta sha’anin tsaro a duniya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta Amurka ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, kasashen duniya da suka mallaki makamin ba su goyi bayan yarjejeniyar ba.

Kasashen da suka mallaki nukiliya sun hada da Amurka da Rasha da Faransa da Birtaniya da China da India da Pakistan da Isra’ila da kuma Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.