rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Sudan Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta janye wa Sudan takunkuman shekaru 20

media
Shugaban Sudan Omar al-Bashir REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah

Gwamnatin Sudan ta yi madalla da matakin da Amurka ta dauka na kawo karshen takunkuman karayar tattalin arziki da ta kakaba ma ta har tsawon shekaru 20.


Sudan ta kuma bukaci Amurka da ta janye kasar daga jerin sunayen kasashen da ta ce, suna tallafa wa ayyukan ta’addanci.

A cewar, Amurka ta dauki matakin janye takunkuman ne saboda ci gaban da Sudan ta samu wajen mutunta hakkin dan Adam.

Daukan matakin na zuwa ne bayan kasashen biyu sun shafe tsawon watanni suna ganawar diflomasiya wadda aka fara ta tun lokacin shugabancin Barack Obama da ya mika wa Donald Trump mulki.

Ana ganin janye takunkuman zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Sudan.