rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Saudiya Iran Qatar Daular Larabawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya ta siyi makaman Dala biliyan 15 daga Amurka

media
Nauyin makamin kakkabo makami mai linzami na Amurka Leah Garton/Missile Defense Agency/Handout via REUTERS

Amurka ta amince ta siyar wa Saudi Arabia makaman kakkabo makamai masu linzami akan farashin Dala biliyan 15.


Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ta ce, cinikin zai habbaka harkar tsaronta da kuma manufofinta na kasashen ketare.

Sanarwar ta kara da cewa, cinikin zai taka rawa dangane da sha’anin trsaro a Saudiya da kasashen yankin Gulf, lura da barazanar da ke kunno kai daga Iran da wasu kasashen duniya.

Tuni dai Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da ke makwabtaka da Saudiya suka siyi wadannan makamai masu kakkabo makamai masu linzami.