rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Mali Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Afrika na shirin gurfanar da Sarkozy na Faransa

media
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy GEORGES GOBET / AFP

Kungiyoyin fara hula da dama ne daga kasashen Afrika suka yanke shawarar gurfanar da tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a gaban kotun Duniya da ke Hauge, bisa zargin cewa shi ne ya jagoranci aikin kashe tsohon shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi, lamarin da kuma ya yi sanadiyyar bazuwar makamai zuwa kasashe da dama na Afirka.


Shahararren mawakin Afrika Tiken Jah Fakoli, shi ne ya jagoranci taron da kungiyoyin suka gudanar a birnin Bamako na kasar Mali.

A zantawarsa da RFI, Fakoli ya ce, lalle ya kamata a hukunta Nicolas Sarkozy saboda da dama daga cikin tsoffin jami’an gwamnatin Gaddafi sun fara magana.

A cewarsa, kisan da aka yi wa Kanar Gaddafi, ba wani abu ba ne face daukar fansa domin huce fushi.

"A sassa da dama na Afrika za ka tarar da makamai da aka wawashe daga Libya bayan kashe Gaddafi, hatta kungiyoyin ‘yan ta’adda sun amfana da wannan kisa domin sun samu dimbin makamai da suka yi amfani da su don wargaza zaman lafiya a Mali da sauran kasashe" in ji Fakoli.