rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump na iya jefa Amurka cikin hadari- Sanata Coker

media
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Joshua Roberts

Daya daga cikin manyan 'yan Majalisar Dattawan Amurka daga Jam’iyyar Republican ya raba hannun riga da shugaban kasar Donald Trump, in da ya ce rashin hankalin shugaban na iya jefa Amurka cikin hadari.


Sanata Bob Coker ya bayyana fadar White House ta shugaban Amurka a matsayin wurin kula da kananan yara, in da ya ke cewa shugaba Trump na iya jefa Amurka cikin yakin duniya na 3 saboda irin halayensa.

Sanata Coker ya bayyana Sakataren Harkokin Wajen kasar, Rex Tillerson da Sakataren Tsaro, Jim Mattis da Babban Hafsa a fadar shugaban kasa, John Kelly a matsayin wadanda ke kare Amurka daga fadawa cikin rikici.

Shugaba Trump ya ce, Sanatan na furta wadannan kalamai ne saboda ya ki goyon bayan sake tsayawa takararsa da kuma nada shi a matsayin Sakataren Harkokin Waje.