Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta yi wa Amurka baraza kan Bisa

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana takaicinsa kan matakin da Amurka ta dauka na daina bai wa ‘yan kasar Bisa, in da ya bukace ta da ta gaggauta janye wannan mataki ko kuma Turkiya ta mayar da martani.

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip erdogan tare da takwaransa na Amurka, Donald Trump
Shugaban Turkiya, Recep Tayyip erdogan tare da takwaransa na Amurka, Donald Trump ©AFP
Talla

Tsamin dagantaka da ya jima tsakanin kasashen biyu duk da cewa suna aiki tare a kungiyar tsaro ta NATO, ya sake bijirowa ne bayan Turkiya ta daure wani ma’aikacin kasar da ke aiki da ofishin jakadancin Amurka a birnin Santanbul.

Shugaba Erdogan ya ce, wannan mataki na dakatar da Bisan abin takaici ne da jakadan Amurka a Ankara zai dauka har ya aiwatar da shi.

Tuni dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiya ta kira jakadanta da ke Amurka gida tare da bukatar Washington ta sauya matsayinta.

A karshen makon da ya gabata ne ofishin jakadancin Amurka a Turkiya ya ce, zai daina bada Bisa ga masu zuwa yawon bude ido da marasa lafiya da ‘yan kasuwa da kuma ma’aikata da dalibai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.