rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wutar daji ta laklume rayuwa a California ta Amurka

media
Ma'aikatan kashe gobara na ci gaba da kokarin kawar da wutar daji a jihar California ta Amurka BERTRAND LANGLOIS / AFP

Wata mahaukaciyar wutar daji mai harsuna sama da 12 ta lakume rayukan mutane akalla 10 tare da lalata daruruwan gidaje a Jihar California da ke Amurka.


Ma’aikatar kashe gobara ta ce, wutar ta lakume eka dubu 73, abin da ya tilasta wa hukumomi kwashe akalla mutane dubu 20 daga gidajensu, yayin da kuma aka ayyana dokar ta baci.

Gwamnan Jihar Jerry Brown ya ce, tuni wutar ta rufe garuruwan Napa da Sonoma da Yuba, yayin da ma’aikatan kashe gobara 410 ke kokarin yaki da ita.

Duk da dai jihar Carlifonia na yawan fama da wutar daji, amma a wannan karo ibtila’in ya tsananta ne saboda yanayi na rani gami da iska mai karfi da ke kadawa.