rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Eminem ya caccaki Trump

media
Mawakin Amurka Eminem REUTERS

Fitaccen mawakin Rapper na Amurka Eminem ya caccaki Donald Trump a salon wakensa inda ya kira shugaban a matsayin babban mai nuna wariyar launin fata.


Eminem ya caccaki Trump ne a wani bidiyo da ya fitar mai tsawon kusan minti 5 inda ya yi waken cikin fushi da zazafan kalamai na nuna kyama da adawa da shugaban na Amurka.

“Wariyar Launin fata ne kawai abin da ya fi kwarewa akai” in ji Eminem a cikin baitikansa.

Sannan mawakin ya ambaci tsohon shugaban Amurka Barack Obama a baitikansa inda ya ce ya fi Trump da ke shirin kaddamar da yakin Nukiliya.

Daga karshe Eminem ya yi kira ga magoya bayansa su bijerewa Trump.

Bidiyon Eminem da ya ke caccakar Trump