rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Libya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU na shirin bude ofishin jakadancinta a Libya

media
Birnin Tripoli na Libya REUTERS/Omar Ibrahim

Kungiyar Kasashen Turai na shirin bude ofishin Jakadancinta a Libya a wani yunkuri na nuna goyan baya ga gwamnatin da ke samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya.


Wani daftarin da ake saran shugabannin kungiyar su amince da shi a taron da za ayi a makon gobe, ya nuna cewar kungiyar na shirin bude ofishinta a Tripoli.

Yanzu haka kasar Italiya da ta yi wa Libya mulkin mallaka ce kawai ke da ofishin jakadanci a Tripoli daga cikin kasashen kungiyar 28.

Kungiyar Turai ta dauke ofishinta daga Tripoli zuwa Tunisia ne a tsakiyar shekarar 2014 sakamakon tsananin tashin hankalin da kasar ta yi fama da shi.