rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

UNESCO Amurka Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta janye daga UNESCO

media
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Yuri Gripas

Amurka ta janye daga hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da kimiya da al’adu a duniya bayan ta zargi hukumar da nuna kyama ga Isra’ila.


Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da janyewar Amurka daga hukumar ta UNESCO a yau Alhamis.

Tun a 2011 Amurka ke adawa da UNESCO inda ta dakatar da ba hukumar tallafi bayan amincewa da ba Falasdinawa wakilci duk da kin amincewar Isra’ila.

Amurka ta fadi a cikin sanarwar da ta aikawa babbar jami’ar UNESCO Irina Bukova cewa za ta ci gaba da bada goyon baya ga muhimman ayyukan hukumar da suka shafi kare gidajen tarihi da ‘yancin jarida da kuma ci gaban ilimi da kimiya.

Amurka wacce tana daya daga cikin kasashen da suka kafa UNESCO, ta taba ficewa a 1984 zamanin shugaba Ronald Reagan kafin 2002 da shugaba George W Bush ya dawo da wakilcin Amurka a hukumar.