rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

UNESCO Majalisar Dinkin Duniya Faransa Qatar Amurka Isra'ila Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Azoulay ta lashe kujerar hukumar UNESCO

media
Audrey Azoulay, sabuwar shugabar hukumar UNESCO AFP PHOTO / PATRICK KOVARIK

An zabi tsohuwar Ministar al’adu ta Faransa, Audrey Azoulay a matsayin sabuwar Darekta Janar ta hukumar bunkasa ilimi, kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya bayan ta doke abokin takararta a zagaye na biyar , wato Hamad Abdul-Aziz al-Kawari na Qatar.


Azoulay mai shekaru 45 za ta kasance mace ta biyu a tarihi da ta jagoranci hukumar UNESCO, yayin da ta samu kuri’u 30 akan al-Kawari da ya samu 28.

Nasarar Azoulay na zuwa ne bayan Amurka da Isra’ila sun sanar da shirinsu na janyewa daga hukumar ta UNESCO saboda tarin matsalolin siyasa da suka addadi hukumar.

Sai dai ana saran sabuwar shugabar za ta yi kokarin shawo kan Amurka da Isra’ila don ganin cewa sun ci gaba da zama mamba.

Al-Kawari ya gaza kai wa ga gaci ne a zaben wanda aka gudanar a birnin Paris na Faransa a jiya jumma’a bayan kasashen yankin Gulf da ke kawance da Saudiya sun ki jefa ma sa kuri’u.